logo

HAUSA

Kumbon Chang’e-6 na kasar Sin ya tattaro giram 1,935.3 na samfura daga yankin duniyar wata mai nisa

2024-06-28 16:55:59 CMG Hausa

Hukumar kula da ayyukan sama jannati na kasar Sin (CNSA) ya ce kumbon bincike na Chang’e-6 na kasar Sin, ya tattaro giram 1,935.5 na samfura daga bangaren duniyar wata mai nisa.

An mika samfuran ga tawagar masu bincike daga kwalejin nazarin kimiyya ta kasar Sin, yayin wani bikin da hukumar CNSA ta shirya yau Juma’a a Beijing. Masu binciken za su gudanar da ayyukan da suka shafi adanawa da tantance samfuran na duniyar wata kamar yadda aka tsara, sannan kuma su kaddamar da aikin bincike.

Na’urar dawowa ta kumbon bincike na Chang’e-6, ta dawo duniyar dan adam ne a ranar 25 ga watan Yuni, dauke da samfuran irinsu na farko, da kumbon ya tattaro daga yankin duniyar wata mai nisa, inda ya sauka a jihar Mongolia ta gida mai cin gashin kanta dake arewacin kasar Sin .  (Fa’iza Mustapha)