Xi ya gabatar da jawabin cika shekaru 70 na ka’idoji 5 na zaman tare cikin lumana tsakanin kasa da kasa
2024-06-28 15:25:08 CMG Hausa
Shugaban kasar Sin Xi Jinpping, ya gabatar da muhimmin jawabi ga taron murnar cika shekaru 70 na ka’idoji 5 na zaman tare cikin lumana tsakanin kasa da kasa.
Ya ce yau shekaru 70 da suka gabata, aka kaddamar da ka’idoji 5 na zaman tare cikin lumana tsakanin kasa da kasa, wanda kuma ya alamta sabon babi da gagarumar nasara a tarihin dangantakar kasa da kasa.
A cewarsa, cikin sama da shekaru 70 da suka gabata, ka’idojin 5 sun kasance ka’idoji na bai daya da ake bayyana ga dangantakar kasa da kasa da tsarin dokokin kasa da kasa. Kuma sun bayar da gudunmawa mai muhimmanci ga ci gaban dan adam.
Ya ce daga cikin kasashen duniya, kasashe masu tasowa sun kasance masu kuzari mai karfi, da taka muhimmiyar rawa wajen inganta ci gaban dan Adam. Yana mai cewa, a wani mafari na sabon tarihi, ya kamata kasashe masu tasowa su kara bude kofofinsu tare da dunkulewa, su kuma hada hannu tare, domin jagorantar gina al’umma mai makoma ta bai daya.
Bugu da kari, shugaba Xi ya ce a yanzu, kasar Sin na gina kasa ta zamani mai tsarin gurguzu a dukkan fannoni da kuma cimma farfadowar kasar ta hanyar zamanintar da kanta. A kuma wannan sabon tafarki, za a ci gaba da hada hannu wajen daukaka ka’idoji 5 na zaman tare cikin lumana da kara yin hada gwiwa da sauran kasashe wajen gina al’umma mai makoma ta bai daya ga daukacin bil adama, tare da bayar da karin sabbin gudunmawa ga kare zaman lafiya da inganta ci gaba a duniya. (Fa’iza Mustapha)