logo

HAUSA

Ministocin tsaron kasashen Sin da Mozambique sun gana a Beijing

2024-06-28 10:23:10 CMG Hausa

Ministan tsaron kasar Sin Dong Jun, ya gana da takwaransa na Mozambique Cristovao Chume, wanda ke ziyara a kasar Sin, jiya Alhamis a birnin Beijing.

Da yake bayyana dangantaka ta kut da kut da kyakkyawan hadin gwiwar dake tsakanin rundunonin sojin kasashen biyu, Dong Jun ya ce a shirye Sin take ta hada hannu da Mozambique wajen aiwatar da matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma da karfafa muhimmiyar dangantakarsu a fannoni daban-daban da kuma daukaka dangantakarsu ta fuskar aikin soji zuwa sabon mataki.

Da yake bayyana abotar dake tsakanin rundunonin sojin kasashen biyu a matsayin dadaddiya, Cristovao Chume ya bayyana fatan bangarorin biyu za su ci gaba da karfafa musaya da kirkiro sabbin bangarorin hadin gwiwa. (Fa’iza Mustapha)