Shugaban Sin Xi Jinping da takwaransa na Venezuela Nicolás Maduro Moros sun yi musayar sakon taya murna
2024-06-28 15:53:56 CMG Hausa
Yau Jumma’a, shugaban Sin Xi Jinping da takwaransa na Venezuela Nicolás Maduro Moros, sun yi musayar sakon taya murnar cika shekaru 50 da kulla huldar diplomassiya tsakanin kasashensu.
Xi Jinping ya yi nuni da cewa, kasashen Sin da Venezuela abokan hulda ne na kwarai masu amincewa da juna da kuma samun ci gaba tare. Kuma Sin tana son hada hannu da Venezuela wajen ci gaba da inganta ma'anar dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakaninsu, tare da sa kaimi ga gina al'umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya ga daukacin bil'adama.
A nasa bangare, Nicholas Maduro ya ce, Venezuela tana goyon bayan kasar Sin sosai wajen kare ikonta na mulkin kasa, kuma tana adawa da duk wani yunkuri na dakile kasar Sin, haka kuma tana son taka rawa wajen aiwatar da shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya da kuma muhimman shawarwari uku dake shafar duk duniya baki daya da shugaba Xi Jinping ya gabatar. (Safiyah Ma)