logo

HAUSA

Ministan shari’ar Nijar ya ja hankali game da yawaitar shan miyagun kwayoyi a kasar

2024-06-26 20:28:53 CMG Hausa

 

Ministan shari’ar jamhuriyar Nijar Alio Daouda ya ja hankali game da yawaitar shan miyagun kwayoyi tsakanin al’umma, yana mai cewa, alkaluman hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasar sun nuna cewa, Nijar ta kama hanyar zama cikin jerin kasashe da jama’arsu ke yawaita shan miyagun kwayoyi.

Yayin da yake tsokacin, albarkacin ranar yaki da fatauci, da shan miyagun kwayoyi ta kasa da kasa da aka yi bikinta a Larabar nan, Daouda ya ce, alkaluman babban ofishin wakilci mai lura da fasa kwaurin miyagun kwayoyi na kasar, sun nuna yadda a shekarar 2023 kadai, aka yi nasarar kwace kimamin kilogiram 77.52 na sinadarar da aka fitar daga tabar wiwi, da tan 10.76 na ganyen tabar wiwi, da kilogiram 61.63 na hodar Iblis.

Ministan ya kara da cewa, samari da matasa ne ke kan gaba, wajen hadarin fadawa illar shan miyagun kwayoyi, kuma gwamnatin kasar za ta yi duk mai yiwuwa wajen aiwatar da tsauraran matakai, na shawo kan kalubalen bazuwa, da shan miyagun kwayoyi a Nijar.  (Saminu Alhassan)