logo

HAUSA

Shirin sauya tsoffin hajoji da sabbi na kasar Sin na taimakawa ga kara sayar da muhimman hajoji

2024-07-01 15:27:11 CMG Hausa

A watan Maris din bana, gwamnatin kasar Sin ta bullo da wani shiri na sauya tsoffin hajoji da sabbi, wanda ke taimakawa sosai ga kara sayar da wasu muhimman hajoji, ciki har da motoci, da na’urori da kayayyakin amfanin gida. Shirin dai ya kasance wani muhimmin bangare na kokarin da kasar Sin take yi, na bunkasa bukatun cikin gida da habaka tattalin arziki.