logo

HAUSA

Gwamnatin Amurka ta yi gargadi kan illolin da kafofin sada zumunta suke haifawa ga matasa da yara

2024-04-06 17:11:10 CMG Hausa

 

Wani jami’in lafiyar kasar Amurka ya tunatar da iyaye a kwanan baya cewa, kila yadda kananan yara da matasa suke amfani da kafofin sada zumunta fiye da yadda suke bukata, kuma kafin sun zama baligai, zai iya haifar musu da illa a lafiyar jikinsu, da tunaninsu, da kuma yadda suke girma yadda ya kamata.

Ma’aikatar lafiya da ba da hidimomin al’umma ta Amurka ta kaddamar da rahoto a kwanan baya, inda ta tunatar da iyayen matasa da kananan yara da su yi taka tsan-tsan kan illolin da kafofin sada zumunta ke haifarwa. Rahoton ya ruwaito cewa, yin amfani da kafofin sada zumunta ya zama ruwan dare tsakanin Amurkawa matasa da kananan yara. Kuma kashi 95 bisa 100 sun saba da yin amfani da kafofin, kana kashi 1 cikin kashi 3 sun ce, suna amfani da kafofin kusan ba tare da tsayawa ba.

Vivek Murthy, shugaban hukumar lafiyar al’ummar Amurka ya bayyana cikin rahoton cewa, ko da yake kafofin sada zumunta suna da amfani ga matasa da kananan yara, wajen kafa tsarin mu’amalar mutane da dai sauransu, amma akwai wasu shaidu da ke nuna yadda kafofin sada zumuntar ke yin barazana ga tunaninsu da jin dadin zamansu.

Dangane da illolin, madam Zhang Chuji, likita da ke aikin a asibitin Tiantan na Beijing ta yi mana karin bayani da cewa, ana baza damuwar kyan surar jiki, da cin abinci fiye da yadda ake bukata, da cutar damuwa, da cin zali wasu, da janyo wasu su jikkata kansa, da sauran abubuwa marasa dacewa da muni da masu ra’ayin rikau a kafofin sada zumunta, wadanda suke haddasa illoli ga matasa da kananan yara yayin da suke muhimmin matakin girma.

Mista Murthy ya yi kira ga masu tsara manufa, da su kyautata ka’idoji masu nasaba da kafofin sada zumunta, kana kamfanonin fasaha su sauke nauyin kimanta illolin da kafofin sada zumuntansu ke haifarwa ga matasa da kananan yara, da kuma rarraba bayanai masu nasaba.

Har ila yau, iyaye su kebe wurin musamman, inda ba a rika amfani da kayan laturoni na zamani a gidajensu ba, a kokarin samar wa ‘ya’yansu wani misali na yin amfani da yanar gizo ta hanyar da ta dace. (Tasallah Yuan)