logo

HAUSA

Yawan Amurkawan da suka kashe kansu ya kafa tarihi a shekarar 2022

2024-04-21 17:20:08 CMG Hausa

 

Cibiyar dakilewa da kandagarkin cututtuka ta kasar Amurka ko CDC, ta gabatar da alkaluma a kwanan baya, wadanda ke cewa a shekarar 2022 kadai, Amurkawa kusan 49,500 sun kashe kansa, adadin da ya karu da kashi 2.6 cikin kashi 100 bisa na shekarar 2021, ya kuma kafa tarihi. Madam Jill Harkavy-Friedman, mataimakiyar shugaba mai kula da harkokin nazari a asusun magance kashe kai a Amurka tana ganin cewa, wani muhimmin dalilin da ya sa hakan shi ne yaduwar bindiga a Amurka.

CDC ta kimanta cewa, a shekarar 2022 mutane dubu 49 da 449 suka kashe kansu, adadin da ya fi na shekarar 2021.

Kaza lika kwatankwancin mutum 14.9 sun kashe kansu cikin duk mutane dubu 100. Adadin ya kafa tarihi na yawan hakan. Kafin hakan, a  shekarar 2018, adadin ya kai mutum 14.2 cikin duk mutane dubu 100.

Xavier Becerra, ministan lafiya da hidimomin al’umma na kasar Amurka ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, Amurkawan da yawansu ya kai kashi 9 cikin 10 ne suke ganin cewa, Amurka na fama da matsalar lafiyar tunani. Alkaluman da CDC ta gabatar sun bayyana dalilan da suka sa hakan.

Masana na ganin cewa, akwai dalilai masu sarkakiya da suka sa wasu ke kashe kansu. Mai yiwuwa ne karuwar yawan masu fama da cutar damuwa, karancin hidimomin kiwon lafiyar tunani da dai sauransu, na haddasa hauhawar adadin masu kashe kansu a shekarun baya-bayan nan a Amurka. Amma madam Jill Harkavy-Friedman, ta yi nuni da cewa, wani muhimmin dalili shi ne yawaitar bindiga a kasar. Tana mai cewa, idan ba a ambato bindiga ba, ta yaya za a tattauna batun kashe kai?

Alkaluman CDC sun nuna cewa, a shekarar 2022 ne fiye da rabin batutuwa masu nasaba da kashe kai a Amurka suna shafar bindiga. Ana kara sayar da bindiga masu dimbin yawa a Amurka. Kashe kai da bindiga ya zama ruwan dare a kasar.

Sakamakon nazarin da jami’ar Johns Hopkins ta kaddamar a kwanan baya ya yi daidai da alkaluman CDC. A cikin nazarin, an tabbatar da cewa, kason yawan masu kashe kansu da bindiga cikin jimillar masu kashe kansu a Amurka a shekarar 2022 ya kai matsayin koli, musamman ma karon farko na yawan matasa bakaken fata da suka kashe kansu da bindiga, ya fi na takwarorinsu fararen fata.

Tun farkon karnin da muke ciki, yawan masu kashe kai na ta karuwa a ko wace shekara a Amurka. Ko da yake adadin ya dan ragu a shekarar 2019 da ta 2020, amma ya ci gaba da karuwa a shekarar 2021 da ta 2022. (Tasallah Yuan)