logo

HAUSA

Habasha ta kaddamar da shirin dakile yaduwar HIV/AIDS

2024-06-12 08:10:45 CMG Hausa

 

Kwanan baya, ma’aikatar lafiyar kasar Habasha ta kaddamar da sabon shirin gwamnati na dakile yaduwar cuta mai karya garkuwar jiki ko AIDS a kasar, a kokarin dakatar da yaduwar cutar a wannan kasar da ke arewa maso gabashin nahiyar Afirka.

A cikin sanarwar da ma’aikatar lafiyar Habasha ta fitar a kwanan baya, ta bayyana cewa, za a shirya wani tsari na hada kan sassa daban daban na kasar nan da shekaru 4 masu zuwa, a kokarin dakile yaduwar cutar AIDS tsakanin al’ummar kasar, da rage yawan sabbin masu kamuwa da cutar, da mutuwar masu kamuwa da cutar.

Ma’aikatar lafiyar Habasha ta yi karin bayani da cewa, tana fatan za a rage yawan masu kamuwa da cutar AIDS da mutum daya cikin duk mutum dubu 10 a duk fadin kasar.

Ma’aikatar ta kuma samar da horo mai zurfi ga masu aiwatar da shirin, ciki har da wakilan da suka fito daga wurare 330, inda aka fi samun yawan masu kamuwa da cutar a kasar.

Bisa alkaluman da asusun kula da al’umma na MDD ya gabatar, an ce, kasar Habasha da ke arewa maso gabashin nahiyar Afirka, ta samu gagarumin ci gaba cikin shekaru 20 da suka gabata, inda ta rage yawan masu kamuwa da cutar ta AIDS zuwa kashi 0.9 cikin kashi 100 a shekarar 2017, a maimakon kashi 3.3 cikin kashi 100 a shekarar 2000, kana yawan mutuwar mutane mai nasaba da cutar AIDS ya ragu zuwa dubu 15 da dari 6 a shekarar 2017, a maimakon dubu 83 a shekarar 2000.

Akwai bambanci sosai a fannin yaki da cuta mai karya garkuwar jiki ko AIDS a sassa daban daban, da kuma al’ummomi daban daban a kasar Habasha a ‘yan kwanakin baya. Asusun kula da al’umma na MDD ya yi karin bayani da cewa, yadda cutar AIDS take yaduwa a biranen Habasha, ya fi kamari sama da yadda cutar take yaduwa a yankunan karkarar kasar da rubi 7.

Alkaluman hukumar WHO sun nuna cewa, ya zuwa shekarar 2022 da ta gabata, mutane miliyan 25.6 a kasashen Afirka sun kamu da kwayar cuta mai karya garkuwar jiki ko AIDS, inda wasu miliyan 20.9 suke samun jinya yadda ya kamata. (Tasallah Yuan)