Kila kara yawan cin kayayyakin lambu masu kwarran ganyaye kullum na iya maganin kamuwa da cutar mantuwa ta Alzheimer's
2024-05-07 07:59:40 CMG Hausa
Masu karatu, ko kun san cutar mantuwa ta Alzheimer's? Wannan cuta wani nau’in ciwon karancin basira ne dake farawa daga matsalar mantuwa, daga bisani ya shafi tunanin mutane, da kwarewar magana, har ma da gudanar da harkokin yau da kullum. Ko da yake har yanzu ba a kai ga gano dalilin dake haifar da cutar, da kuma dabarar shawo kanta ba, amma masu nazari daga kasar Amurka sun gano cewa, kila kara yawan cin kayayyakin lambu masu kwarran ganyaye kullum na iya maganin kamuwa da cutar.
Masu nazari daga jami’ar Rush ta Amurka sun bayyana ciki rahoton nazarinsu cewa, daga shekarar 2014, sun tattara bayanai masu nasaba da masu aikin sa kai 581, wadanda suka riga mu gidan gaskiya, wadanda suka shiga shirin nazarin da aka fara daga shekarar 1997 a jami’ar, dangane da rike abubuwa a kwakwalwa da kuma tsufa. Wadannan bayanai sun hada da al’adar masu aikin sa kan ta cin abinci yayin da suke raye. Bayan masu aikin sa kan sun mutu, sun bayar da gawawwakinsu kyauta domin yin bincike. Masu nazarin sun yanka kwakwalwarsu, sun kuma gano cewa, sinadaran Amyloid β-protein da aka samu a kwakwalwar wadanda su kan ci soyayyen abinci, da kayan abinci masu zaki, da taune-taune da lashe-lashe, sun fi na wadanda su kan ci kayayyakin lambu masu kwarran ganyaye yawa.
Taruwar yawan sinadaran Amyloid β-protein da aka samu a kwakwalwa, na daya daga cikin alamun kamuwa da cutar Alzheimer's.
Masu nazarin sun yi nuni da cewa, kayayyakin lambu masu kwarran ganyaye cike suke da Bitamin, sinadaran ma’adinai, sinadaran Flavonoids da dai sauransu, wadanda suke iya rage kumburi, da karfafa lafiyar jiki, da ma amfanar da lafiyar kwakwalwa.
Sun kuma ba da shawarar cewa, yana da kyau a ci kayayyakin lambu masu kwarran ganyaye sau daya a ko wane mako, kuma launin ganyayen kayayyakin lambun ya zama mai kore sosai, domin sun fi amfani ga lafiyar jiki. Ban da haka kuma, ‘ya’yan itatuwa dangin Berry, su ma suna amfani ga lafiyar kwakwalwa, don haka kamata ya yi a ci irinsu a kalla kwanaki 5 a ko wane mako.
Dangane da abincin da kamata ya yi a ci domin maganin cutar ta Alzheimer's, madam Zhang Chuji, likita da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing, ta yi mana karin haske da cewa, ya kamata a dan kyautata tsarin abinci na yau da kullum. Alal misali, a kara yawan cin kayayyakin lambu masu kwarran ganyaye, da ‘ya’yan itatuwan Berry, da kayayyakin abinci na hatsi, man zaitun, da kifi, a kokarin jinkirta kamuwa da cutar ta Alzheimer's, ko kuma rage barazanar kamuwa da cutar bayan an tsufa. (Tasallah Yuan)