logo

HAUSA

Barazanar kadaici ga lafiya tamkar shan karan taba 15 ne a kowacce rana

2024-04-15 08:31:53 CMG Hausa

 

Shugabar hukumar kula da lafiyar al’umma na kasar Amurka mista Vivek Murthy, ya bayyana a kwanan baya cewa, kadaici, sabuwar barazana ce da Amurkawa suke fuskanta. Barazanar kadaici ga lafiya tamkar shan karan taba 15 ne a kowacce rana. Kuma babu wani abu da zai maye gurbin yin mu’amala tsakanin mutane fuska da fuska.

Rahoton da hukumar ta gabatar a kwanan baya ya nuna cewa, kusan rabin Amurka baligai suna fama da kadaici. Bincike ya shaida cewa, a cikin gwamman shekaru da suka gabata, sannu a hankali Amurkawa suna rage mu’amala da iyalansu, da unguwanni da kungiyoyin addinan su. Kaza lika karin mutane suna fama da kadaici.

Kamfanin dillancin labaru na Associated Press, wato AP a takaice ya ruwaito cewa, a cikin shekaru 60 da suka wuce, yawan iyalai masu mutum daya tak ya ninka sau daya.

Bayan barkewar annobar cutar numfashi ta COVID-19 har zuwa yanzu, irin wannan yanayi ya kara yin muni. Alkaluma sun nuna cewa, a shekarar 2020, Amurkawa na shafe mintuna 20 ne kacal a kowacce rana suna tare da abokansu, amma shekaru kusan 20 kafin shekarar ta 2020, tsawon lokacin ya kai mituna 60. In an kwatanta su da sauran Amurkawa, ‘yan shekaru tsakanin 15 zuwa 24 a duniya, wannan rukuni sun fi fuskantar matsalar kadaici.

Rahoton ya ci gaba da cewa, matsalar kadaici tana kara barazanar mutuwa da kusan kashi 30 cikin 100. Tabbas, wadanda ba sa mu’amala da al’umma sun fi fuskantar hadarin shanyewar barin jiki, da kamuwa da ciwon zuciya. Haka kuma, matsalar ta kadaici na kara wa mutane barazanar kamuwa da cutar damuwa, da cutar “Alzheimer's”, wani nau’in ciwon karancin basira da dake farawa daga matsalar mantuwa, daga bisani ya shafi tunanin mutane, da kwarewar magana, har ma da gudanar da harkokin yau da kullum. Murthy yana mai cewa, barazanar mutuwa sakamakon kadaici ta fi ta matsalar kiba, tamkar dai ta shan karan taba 15 ne a kowacce rana.

Don haka Murthy ya yi kira ga shugabanni, makarantu, kamfanonin fasaha, da unguwanni da su samar da dabarar karfafa gwiwar mutane, wajen yin mu’amala da juna. Wasu na ganin cewa, ci gaban fasaha ya tsananta matsalar kadaici. Rahoton ya ruwaito sakamakon wani nazari da cewa, wadanda suke amfani da kafofin sada zumunta har awoyi 2 ko kuma fiye da haka a kowacce rana sun fi jin kadaici da har ninki 1, gwargwadon wadanda suke amfani da kafofin mituna 30 a kowacce rana. Murthy ya ce, babu wanda zai maye gurbin yin mu’amala tsakanin mutane fuska da fuska. (Tasallah Yuan)