logo

HAUSA

Cin abinci mai cike da sinadarin Magnesium na kare mutane daga kamuwa da cutar karancin basira

2024-05-13 15:33:32 CMG Hausa

 

Jami’ar kasar Australia ta ba da wata sanarwa a kwanan baya cewa, nazarin da jami’ar ta gudanar ya gano cewa, yayin da mutane suka tsufa, yawaita kara cin alayyaho, da gyada, da dangin ta, da sauran kayayyakin abinci masu cike da sinadarin Magnesium a zaman yau da kullum, yana amfani ga lafiyar kwakwalwa, da rage hadarin kamuwa da cutar karancin basira.

Masu nazarin sun tattara bayanan da suka shafi ‘yan kasar Birtaniya fiye da dubu 6, ‘yan tsakanin shekaru 40 zuwa 73, wadanda suka amsa tambayoyi sau 5 cikin watanni 16. A cikin mabambantan kayayyakin abinci iri iri har 200, masu nazarin sun mai da hankali kan wasu masu cike da sinadarin Magnesium, kamar kayayyakin lambu masu kwarran ganyaye, da wake, da gyada da danginta, da kayayyakin abincin hatsi, a kokarin samun matsakaicin yawan sinadarin Magnesium da ake shigarwa cikin jikin dan Adam yayin da ake cin abinci.

Masu nazarin sun gano cewa, a kan shigar da sinadarin na Magnesium na miligram 350 a ko wace rana. Amma idan an kara shigar da sinadarin har fiye da miligram 550 a ko wace rana, kwakwalwar mutane kan kara tsawon kuruciya da shekara guda, yayin da shekarunsu suka kai 55 a duniya.

Masu nazarin sun bayyana cikin sanarwar cewa, nazarinsu ya nuna cewa, kila kara shigar da sinadarin Magnesium da kashi 41 cikin 100 cikin jikin dan Adam, yana iya rage koma bayan kwakwalwa sakamakon tsufa, ta yadda za a rage hadarin kamuwa da cutar karancin basira, ko kuma jinkirta kamuwa da cutar.

Dangane da lamarin, madam Zhang Chuji, likita da ke aiki a asibitin Tiantan na Beijing ta yi karin bayani da cewa, yadda mutane suke kara shigar da sinadarin Magnesium cikin abincinsu na yau da kullum tun suna da kuruciya, yana taimakawa wajen dakile kamuwa da cututtukan koma bayan kwakwalwa, da raguwar kwarewar fahimta. Don haka ya kamata tsoffi, da kanana, da ma matsakaita, su mai da hankali kan shigar da sinadarin na Magnesium cikin abincinsu na yau da kullum.

Alkaluma sun nuna cewa, bisa kiyasi, yawan masu fama da cutar karancin basira zai karu zuwa miliyan mutum 150 a shekarar 2050 a duk fadin duniya, daga miliyan 57 da dubu 400 da aka samu a shekarar 2019, lamarin da zai kara haifar da babban matsin lamba kan lafiyar al’umma, da sashen ba da hidimomin al’umma, da baki dayan tattalin arzikin duniya. (Tasallah Yuan)