logo

HAUSA

Cin makwalashe na iya haifar da koma baya ga amfanin da abinci mai gina jiki ke yi a jikin dan Adam

2024-05-21 10:13:29 CMG Hausa

 

Wadanda suka mai da hankali kan lafiyar kansu su kan sa muhimmanci kan abincin yau da kullum, a kokarin samun daidaiton abubuwa masu gina jiki isassu ba tare da samun kiba ba. Nazarin da aka gudanar a kasar Birtaniya ya gano cewa, wasu wadanda suke mai da hankali kan abinci mai gina jiki su kan kau da kai daga illolin makwalashe. Yadda rubu’in ‘yan Birtaniya suke cin makwalashe, yana haifar da koma baya ga amfanin da abinci mai gina jiki ke yi a jikinsu.

Masu nazari daga kwalejin sarki wato King's College ta jami’ar London dake kasar Birtaniya, sun amince da hakan ne bayan sun yi nazari kan al’adar mutane 854, dangane da yadda suke cin abinci.

Wadannan mutane sun shiga babban nazarin abubuwa masu gina jiki da wasu jami’o’in kasashen Amurka, da Birtaniya, da Sifaniya da Sweden suka gudanar cikin hadin gwiwa. Wasu kashi 95 cikin kashi 100 ne suke cin makwalashe, har sau 2.28 a ko wace rana. Makwalashen da a kan ci su ne biskit, ‘ya’yan itatuwa, da gyada da danginta, da cukui, da man shanu, da kyak na kwababbiyar fulawa da aka hada da madara da mai, da abincin oatmeal ko sandunan hatsi.

Abin da ya kamata a lura da shi shi ne, wasu kashi 26 cikin kashi 100 suna cin abinci ta hanyar da ta dace, amma ba sa maida muhimmanci kan makwalashe masu dacewa.

Masu nazarin sun gano cewa, in an kwatanta da wadanda ba sa cin makwalashe ko kadan, ko kuma makwalashe marasa dacewa, wadanda su kan ci gyada da danginta, da danyun ‘ya’yan itatuwa, da sauran makwalashe masu dacewa, nauyin jikinsu yana dacewa. Haka kuma, makwalashe marasa dacewa, kamar kayayyakin abinci da aka sarrafa su sosai da masu zaki, su kan sanya mutane su ji yunwa, kuma suna da alaka da matsalar kiba da cututtukan jijjiyoyin zuciya.

Har ila yau, lokacin cin makwalashe yana yin tasiri ga lafiyar mutane. Don haka bai dace ba a ci makwalashe bayan karfe 9 na dare. Wata kila saboda kokarin daidai wannan lokaci, mutane kan zabi kayayyakin abinci masu kunshe da kitse, zaki, da kuma wadanda suke bai wa mutane karfi sosai.

Masu nazarin sun yi bayani da cewa, la’akari da mutanen da yawansu ya kai kashi 95 cikin kashi 100 suna cin makwalashe, kana ‘yan Birtaniya suna samun rubu’in karfi daga makwalashe, ya fi kyau a ci ‘ya’yan itatuwa, gyada da danginta da dai sauransu, a maimakon biskit, da kyak da soyayyen dankali, a kokarin kiwon lafiya. (Tasallah Yuan)