logo

HAUSA

WHO: Farfadowar tsarin kiwon lafiyar Afirka ya dogara da samun isasshen makamashi

2024-06-05 16:17:46 CMG Hausa

 

Hukumar kiwon lafiyar kasa da kasa WHO, ta bayyana a yayin wani taron dandalin tattaunawa da aka gudanar ta kafar bidiyo a kwanan baya cewa, game sassa masu yawa na cibiyoyin kiwon lafiya da wutar lantarki a yankunan karkarar kasashen kudu da hamadar Saharar Afirka, shi ne ginshikin bunkasa ikon nahiyar na shawo kan barkewar cututtuka.

Salvatore Vinci, mai bai wa hukumar WHO shawara dangane da makamashi mai dorewa, ya yi nuni da cewa, tabbatar da kiwon lafiyar daukacin al’ummomin kasashen Afirka, da yawancin kasashe masu tasowa a duniya, ya dogara ne ga samarwa ababen kiwon lafiya wutar lantarki, ta yadda za a adana allurar rigakafin cuta yadda ya kamata, da yin amfani da na’urorin tantance kamuwa da cututtuka, da na’urorin ceton rayukan mutane.

Vinci ya ci gaba da cewa, samun makamashi, yana kara azamar samun kyawawan hidimomin kiwon lafiya a nahiyar Afirka. Ya kalubalanci gwamnatocin kasa da kasa, masu zuba jari, da masu samar da tallafin kudi da su rage gibin da ke akwai ta fuskar samun makamashi, ta hanyoyin tattara kudade, da tsara manufofi, da sa ido da yin kwaskwarima.

Jami’in ya yi karin bayani da cewa, a kasashen kudu da hamadar Saharar Afirka, ba a samar wa na’urorin kiwon lafiya da yawansu ya kai kashi 15 cikin dari wutar lantarki ba tukuna, lamarin da ya tauye kokarin da ake yi na daidaita matsalolin da suke biyo bayan shiga talauci da sauyin yanayi.

A halin yanzu, ana samar da wutar lantarki ta hasken rana a sassan kiwon lafiya a wurare daban daban na Afirka, inda ta hakan ake kyautata kulawa da masu juna biyu yadda ya kamata, da kuma yi wa jarirai da kananan yara allurar rigakafi, lamarin da ya taimaka sosai wajen rage mutuwar masu juna biyu, da jarirai sabbin haihuwa a nahiyar.

Cibiyar nazarin albarkatun kasa da kasa, kungiyar nazari ce mai zaman kanta, wadda ke kara azama kan makamashi mai dorewa, kuma ita ce ta kira wannan taro na dandalin tattaunawar, inda masu tsai da kuduri, da kwararru suka tattauna yadda kasashe maso tasowa suke kokarin samun isasshen makamashi, da kuma samar wa al’ummominsu hidimomin kiwon lafiya masu inganci.

Vinci ya bayyana cewa, sakamakon amfani da hasken rana, da karfin iska, da sauran nau’ikan makamashi masu tsabta, ya sa kasashe maso tasowa a Afirka cin gajiyar farfadowar tsarin kiwon lafiya, yayin da suke daidaita matsalolin da suka biyo bayan sauyarwar yanayi. (Tasallah Yuan)