logo

HAUSA

Babban jami’in JKS ya gana da wata tawagar alkalai daga Afrika

2024-06-26 10:21:55 CMG Hausa

Shugaban hukumar kula da harkokin siyasa da shari’a ta kwamitin kolin JKS, Chen Wenqing, ya gana da wata tawagar manyan alkalai daga kasashen Afrika, jiya Talata a birnin Beijing.

Yayin ganawar, Chen Wenqing, wanda kuma mamba ne na ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, ya ce cikin shekarun baya-bayan nan, kasashen Sin da Afrika sun cimma matsaya kan batutuwa da dama da suka shafi raya hadin gwiwar manyan tsare-tsare a tsakaninsu da gina al’ummar Sin da Afrika mai makoma ta bai daya da tsara shirin raya hadin gwiwarsu mai dogon zango.

Ya ce a shirye kasar Sin take ta hada hannu da kasashen Afrika wajen aiwatar da matsayar da suka cimma da shugabanninsu, da zurfafa musayar ra’ayi game da dangantakarsu, musammam ingantaccen hadin gwiwa a fannin shari’a.

A nasu bangare, mambobin tawagar sun ce za su inganta musaya da koyo daga juna tsakanin Sin da Afrika, kan harkokin shari’a. (Fa’iza Mustapha)