Me ya sa gasar cin kofin Turai ta fi son yin hadin gwiwa da kamfanonin kasar Sin
2024-06-26 12:56:56 CMG Hausa
A halin yanzu, ana gudanar da gasar cin kofin Turai wato UEFA Euro 2024, wadda ke jan hankulan masu sha’awar wasan kwallon kafa na kasa da kasa. A yayin da ake gudanar da irin wannan gasa ta koli, a kan fitar da muhimman labarai na bunkasuwar tattalin arzikin kasashen duniya. A matsayin gasar wasannin kwallon kafa dake kan matsayin koli, wadda aka gudanar bayan annobar cutar COVID-19, gasar cin kofin Turai ta wannan karo tana da manyan iyayen tafiya guda 13, wadanda aka fi sani da abokan hadin gwiwarta na kasashen duniya. Cikin wadannan manyan iyaye tafiya guda 13, akwai na kasar Sin guda 5, hakan ya sa, Sin ta kasance kasar da gasar cin kofin Turai ta fi samun iyayen tafiya cikin gasar ta wannan karo da ma wanda ya gabata.
A gasar bana, iyayen tafiya guda biyar daga kasar Sin sun hada da sana’o’in samar da na’urorin wutar lantarki masu kwakwalwa, da motoci masu aiki da wutar lantarki, da salula masu kwakwalwa, da masu gudanar da harkokin ciniki ta yanar gizo tsakanin kasa da kasa, gami da sana’ar nazarin fasahohin biyan kudi da sauransu. Dukkansu suna sahun gaba cikin sabbin sana’o’in dake samun bunkasuwa da sauri a kasashen duniya.
Cikin ’yan shekarun nan, wasu kamfanonin kasar Sin dake kan gaba a fannoninsu, sun kafa cibiyoyin nazari da masana’antu a kasashen waje, lamarin da ya samar da guraben ayyukan yi ga kasashen da abin ya shafa, tare da ya ba da gudummawar kyautata fasahohinsu. Wadannan kamfanonin suna ci gaba da sabunta kayayyakinsu, yayin da suke kyautata tsarin gudanarwa da ayyukansu, domin samar wa masu sayyaya na kasashen duniya kyawawan kayayyaki da hidimomi masu inganci, kuma masu kare muhalli. Haka kuma, sun shiga kasuwannin duniya, yayin da suke gasa da kamfanonin kasa da kasa cikin yanayin adalci, bisa tunanin bude kofa ga waje.
A halin yanzu, irin babbar gasar dake jan hankulan jama’ar kasashen duniya kamar gasar cin kofin Turai, suna maraba da kamfanonin kasar Sin, ba kawai domin kamfanonin kasar Sin suna da kudi ba, domin suna amincewa da kasar Sin da yadda take yin kwaskwarimar tattalin arziki a cikin gida, domin sa kaimi ga kamfanonin kasar su yi kirkire-kirkire, da kuma ba da jagoranci ga kasashen duniya wajen sabunta fasahohinsu. Kamar yadda wasu masanan tattalin arzikin kasashen duniya suka bayyana, ya kamata iyayen tafiya na irin wannan gasar da take da tasiri ga al’ummomin kasa da kasa, su kasance daga kamfanonin dake iya alamta bunkasuwar tattalin arzikin duniya, da ma wadanda ke yin muhimmin tasiri ga kasashen duniya. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)