logo

HAUSA

Sin ta yi watsi da zargin jakadan Amurka na haifar da cikas a fannin musaya tsakanin sassan biyu

2024-06-26 21:10:20 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta ce ba gaskiya ba ne zargin da jakadan Amurka a Sin Nicholas Burns ya yi, cewa wai Sin din ce ta dakatar da musaya tsakanin bangarorin biyu. Mao Ning ta yi kira ga bangaren Amurka, da ya dauki matakai masu karfi na yayata musaya da Sin.

Mao ta kara da cewa, a yanzu haka ana gudanar da bikin matasan Sin da Amurka na bana, mai taken "Bond with Kuliang” a birnin Fuzhou na lardin Fujian, wanda shi ne biki irinsa mafi girma, kana mafi tattaro matasa daga sassa daban daban, dake yin musaya tsakaninsu, tun bayan kafuwar dangantakar diflomasiyya tsakanin Sin da Amurka.

Jami’ar ta kuma jaddada cewa, ba Sin ce ke haifar da tarnaki a fannin musayar al’adu tsakanin sassan biyu ba, Amurka ce ke aikata hakan. Amurka na fakewa da batun tsaron kasa wajen muzgunawa, da yi wa dalibai Sinawa tambayoyi, da ma maido da wasunsu gida daga Amurka, wanda hakan ke matukar haifar da illa ga wadanda lamarin ke shafa.

Ta ce, "Muna fatan bangaren Amurka zai yi aiki tare da Sin wajen yayata musaya tsakanin jama’ar sassan biyu da ta al’adunsu, ta hanyar aiwatar da kwararan matakai, da ingiza tsarin ci gaban dangantakar sassan biyu bisa daidaito.  (Saminu Alhassan)