Shugaba Xi na kasar Sin ya amsa wasikar da mutanen gundumar Jingning suka aika masa
2024-06-26 16:34:48 CMG Hausa
A kwanan baya, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya amsa wata wasika da jama'a da wasu jami'ai na gundumar Jingning ta kabilar She mai cin gashin kanta, dake karkashin birnin Lishui na lardin Zhejiang na kasar Sin, suka aika masa. A cikin wasikarsa, shugaba Xi ya taya mutanen Jingning murnar cika shekaru 40 da kafuwar gundumar, gami da bayyana kyakkyawan fata kan makomar gundumar a nan gaba.
An kafa gundumar Jingning ne a shekarar 1984, wadda ta kasance gundumar kabilar She mai cin gashin kanta daya tilo ta kasar Sin. A kwanakin baya, wasu jami'an gwamnatin gundumar sun aike wa shugaba Xi Jinping wasika, a madadin daukacin mutanen wurin, don bayyana nasarorin da aka cimma a gundumar cikin shekaru 40 da suka wuce, gami da babban burin da suke da shi na mai da gundumarsu abin koyi ga sauran wuraren kasar, a fannin wadatar da al'umma. (Bello Wang)