logo

HAUSA

Kasar Sin ta yi watsi da kalaman Amurka game da ka’idojin hukunta masu neman ballewar Taiwan

2024-06-25 21:43:42 CMG Hausa

Kasar Sin a yau Talata ta yi watsi da Allah wadai da kasar Amurka ta yi kan ka'idojinta na yanke hukuncin laifuka kan 'yan aware masu ra’ayin rikau wadanda suka aiwatar da matakan neman ‘yancin Taiwan ko kuma tunzura a nemi ‘yancin Taiwan, tare da nuna adawa mai tsanani.

Dangane da kalaman mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amurka Matthew Miller game da ka'idojin, inda ya kira matakin kasar Sin a matsayin "mai tayar da hankali da kawo rikici," kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning a taron manema labarai da aka saba yi ta ce, al'ada ce ta yau da kullum ga kasashen duniya su yi amfani da matakan shari'a na miyagun laifuka don hukunta miyagun mutanen da suka nemi ballewa, kuma babu wani daga waje da ke da ikon cewa komai a kan hakan. (Yahaya)