logo

HAUSA

Bangaren dawowa na kumbon Chang’e-6 ya dawo doron duniya

2024-06-25 16:05:16 CMG Hausa

Da misalin karfe 2 da minti 7 na yammacin yau Talata 25 ga wata, bangaren dawowa dauke da samfuran duniyar wata mai nisa na kumbon Chang’e-6 ya sauka lafiya a wani yankin dake gundumar Siziwang a jihar Mongoliya ta gida mai cin gashin kanta ta kasar Sin. A madadin kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, da majalisar gudanarwa, gami da kwamitin koli na sojan kasar, sakatare-janar na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, wanda kuma shi ne shugaban kasa, kuma shugaban kwamitin koli na sojan kasar, Xi Jinping, ya aike da sako zuwa ga babbar hedikwatar dake jagorantar aikin binciken duniyar wata na Chang’e-6 gami da baki daya ma’aikatanta, don taya su murna tare da jinjina musu.

Sakon shugaba Xi ya ce, kumbon Chang’e-6 ya yi nasarar dauko samfura daga duniyar wata mai nisa, har bangren dawowarsa ya dawo doron duniyarmu, al’amarin da ya kasance irinsa na farko a tarihin dan Adam, kana, wata babbar nasara da Sin ta samu a fannin raya kasa mai karfin binciken sararin samaniya da karfin kimiyya da fasaha. Daga shekaru 20 da suka gabata, zuwa yanzu, gaba dayan ma’aikata masu aikin binciken duniyar wata suna himmatuwa wajen gudanar da aiki, da cimma manyan nasarori, har suka kai ga lalubo hanyar binciken duniyar wata mai inganci da samar da moriya. Shugaba Xi ya kara da cewa, kasar Sin gami da jama’arta ba za su manta da babbar gudummawar da ma’aikatan suka bayar ba har abada. (Murtala Zhang)