An yi taron manyan jami’an kasashen kahon Afirka kan zaman lafiya a Beijing
2024-06-25 11:37:53 CMG Hausa
An yi taron manyan jami’an kasashen kahon Afirka kan zaman lafiya karo na biyu jiya Litinin 24 ga wata a Beijing, inda mataimakin ministan harkokin wajen Sin, Chen Xiaodong, da manzon musamman kan harkokin kahon Afirka na ma’aikatar harkokin wajen kasar, Xue Bing, da wakilai daga ma’aikatar kasuwanci da hukumar inganta hadin-gwiwar kasa da kasa ta fuskar ci gaba ta kasar Sin, gami da manyan jami’an ma’aikatun harkokin wajen kasashen Habasha, da Djibouti, da Kenya, da Somaliya, da Sudan ta Kudu, da Sudan da Uganda, da jami’an diflomasiyyarsu dake kasar Sin, suka halarci taron.
A jawabin da ya gabatar a wajen bikin bude taron, Chen Xiaodong ya ce, tun bayan bullo da “tunanin raya yankin kahon Afirka cikin lumana” sama da shekaru biyu da suka gabata, zuwa yanzu, kasar Sin da kasashen kahon Afirka na maida hankali kan wasu manyan burika uku, wato zaman lafiya, da ci gaba, da tafiyar da mulki yadda ya kamata, domin samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin. Ya ce kasar Sin na fatan kokari tare da kasashen kahon Afirka, domin raya yankin ta yadda zai zama wuri mai zaman lafiya da ci gaba da wadata, da kara raya al’ummomin Sin da Afirka masu kyakkyawar makoma ta bai daya. (Murtala Zhang)