Ra’ayin kasashe biyu da mahukuntan Taiwan suka bayar ya shaida yunkurin ‘yan aware na Taiwan
2024-06-24 20:12:34 CMG Hausa
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, mahukuntan Taiwan sun bayar da ra’ayin kasashen biyu, wanda ya shaida yunkurin ‘yan aware na Taiwan, babu shakka za a yi adawa da wannan ra’ayi, kana ba zai canja yadda kasashen duniya suke goyon bayan ka’idar Sin daya tak a duniya ba.
Ban da wannan kuma, Mao Ning ta bayyana cewa, kasar Amurka ta sayarwa yankin Taiwan na kasar Sin makamai, hakan ya saba wa ka’idar Sin daya tak a duniya, da kuma sanarwar hadin gwiwa guda uku tsakanin Sin da Amurka, da tsoma baki kan harkokin cikin gida na kasar Sin, da kuma kawo illa ga ikon mallaka da cikakken yankin kasar Sin. Kasar Sin ta dauki mataka bisa doka na kayyade kamfanoni da manyan jami’ansu da suka shiga aikin sayar da makamai ga yankin Taiwan. (Zainab Zhang)