Sin za ta kara wasu kasashe cikin manufar yada zango ba tare da biza ba da kara yawan jirage masu shigowa
2024-06-24 19:53:33 CMG Hausa
Kasar Sin za ta kara wasu kasashe cikin manufar yada zango a kasar ba tare da biza ba da kuma kara yawan zirga-zirgar jiragen sama daga kasashen da ke da yawan fasinjoji masu shigowa kasar, a kokarin inganta matakan shiga da fita daga kasar, kamar yadda wata sanarwa daga kwamitin koli na tsara shirin raya tattalin arzikin kasar Sin ya bayyana a yau Litinin.
Sanarwar wadda kwamitin kula da yin kwaskwarima a gida da raya kasar Sin da wasu hukumomin gwamnati hudu suka bayar tare ta ce, don kara saukaka yanayin tafiye-tafiye ga masu yawon bude ido a ketare, kasar Sin za ta kaddamar da karin kayayyaki da hidimomi masu inganci.
Ta kuma ta ba da shawarar hada hidimar harsuna da dama cikin taswira da manhajojin zirga-zirga da kuma kyautata hidimar kiran motar haya.
A bangaren ayyukan biyan kudi kuma, kasar Sin za ta sa kaimi ga karbuwar katunan banki na ketare a wurare da shaguna daban daban, a kokarin ganin masu yawon bude ido na ketare sun samu sauki wajen cin abinci, samun wurin kwana, sufuri, sayen tikiti, da yin odar kaya a kasar, kamar yadda sanarwar ta bayyana. (Yahaya)