logo

HAUSA

Kasar Sin na matukar adawa da kudurin dokar Amurka na takaita zuba jari a kasar Sin

2024-06-24 14:05:38 CMG Hausa

Ma’aikatar kula da cinikayya ta kasar Sin, ta bayyana matukar adawa, bayan Baitul-malin Amurka ta sanar da kudurin dokar takaita zuba jari a kasar Sin, ranar Juma’ar da ta gabata.

Kakakin ma’aikatar ya bayyana cewa, ya kamata Amurka ta girmama dokokin kasuwa da ka’idojin takara cikin adalci, ta daina siyasantarwa da amfani da batutuwan cinikayya da tattalin arziki a matsayin makami. (Fa’iza Mustapha)