logo

HAUSA

Ministan harkokin wajen Nijeriya: Dangantakar Sin da Nijeriya na da muhimmanci a fannoni daban daban

2024-06-23 16:57:05 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen Nijeriya dake ziyarar a kasar Sin, Amb. Yusuf Maitama Tuggar, ya bayyana muhimmancin dangantakar Sin da Nijeriya ta fuskar kirkiro ayyukan yi ga matasa da cinikayya da gine-ginen ababen more rayuwa. 

Ministan ya bayyana haka ne yayin zantawarsa a yau Lahadi da wakilan sashen Hausa na gidan rediyon kasar Sin.

Ya kuma kara da cewa, Nijeriya tana son fadada dangantakarta da Sin, musamman a fannonin cinikayya da hakar ma’adinai.