logo

HAUSA

Kasar Sin ta samu gagarumin ci gaba a jadawalin matsayin takara a fannin kasuwanci na kasa da kasa

2024-06-22 17:16:33 CMG Hausa

Kasar Sin ta samu gagarumin ci gaba a jadawalin matsayin takara tsakanin kasa da kasa na shekarar 2024, sabo da karfin kuzarin tattalin arzikinta.

Arturo Bris, daraktan cibiyar tantance matsayin takara tsakanin kasashe ta kwalejin nazarin harkokin kasuwanci ta kasa da kasa (IMD), shi ne ya bayyana haka yayin wata hira ta kafar bidiyo da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a ranar Talata.

Sabon jadawalin matsayin takarar wanda kwalejin IMD ta fitar ranar Talata, ya nuna cewa, Singapore ita ce kasar dake kan gaba wajen takara a duniya, yayin da kasar Sin ta rage tazarar da aka bata, inda ta tsallake matakai 7, saboda karfin farfadowar tattalin arzikinta bayan annobar COVID-19.

Arturo Bris ya kara da cewa, yanzu kasar Sin ta kai matsayi na 14 bayan ta kasance a na 21 a bara. Yana mai cewa, hakan ya samu ne dalilin karfin kuzarin tattalin arzikinta bayan annobar COVID-19.

Jadawalin matsayin takara na duniya na 2024, ya nuna kasar Switzerland a matsayi na biyu, sai Denmarka a matsayi na 3.

Ya kuma nuna cewa, kasashe masu tasowa na cimma matsayin manyan kasashe, musamman a fannonin kirkire-kirkire da amfani da fasahohin zamani da baza komar tattalin arziki. (Fa’iza Mustapha)