logo

HAUSA

Ministocin harkokin wajen Sin da Najeriya sun gana a Beijing

2024-06-22 16:51:06 CMG Hausa

Memban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar, Wang Yi, ya yi shawarwari tare da ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Maitama Tuggar, jiya Jumma’a a Beijing.

Wang Yi ya ce, Najeriya babbar kasa ce a Afirka dake taka muhimmiyar rawa a fannoni daban-daban, kuma tana da matukar muhimmanci a cikin harkokin diflomasiyyar kasar Sin, gami da mu’amalarta da kasashen Afirka. Ya ce raya dangantakar kasashen biyu da kyau, ya dace da muradun al’ummominsu baki daya, kuma zai kafa wani kyakkyawan misali ga raya dangantakar kasar Sin da kasashen Afirka. Haka kuma, kasar Sin na fatan kasashen biyu za su ci gaba da marawa juna baya, da neman cimma moriya tare, da kiyaye zaman adalci da daidaito, tare da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, don neman ci gaba cikin hadin-gwiwa, da ciyar da dangantakar Sin da Najeriya, har ma da Afirka, zuwa sabon matsayi.

A nasa bangaren, Yusuf Maitama Tuggar ya ce, Najeriya za ta ci gaba da yin tsayin daka kan manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, kana, tana fatan inganta mu’amala da manyan jami’an gwamnatin kasar Sin, da zurfafa tuntubar juna, da kara fadada hadin-gwiwarsu. Ya ce Najeriya tana kuma fatan hada kai da kasar Sin, don ingiza hadin-gwiwar kasashe masu tasowa, da tsayawa ga ra’ayin bunkasuwar bangarori daban-daban a duniya, da tabbatar da zaman adalci da tsare gaskiya a duniya.

Har wa yau, jami’an biyu sun kuma halarci cikakken zama na farko na kwamitocin gwamnatocin Sin da Najeriya, wanda aka yi jiya Jumma’a a Beijing, inda suka saurari rahotannin da kwamitin bangarori daban-daban na kasashen biyu suka gabatar, ciki har da siyasa, da diflomasiyya, da al’adu, da yawon shakatawa, da tattalin arziki, da cinikayya, da sana’ar noma, da tsaro da sauransu, tare kuma da tsara shirye-shiryen hadin-gwiwar kasashen biyu a nan gaba.

Wang Yi ya bayyana cewa, kwamitin gwamnatocin kasashen Sin da Najeriya, ya kasance irinsa na farko da kasar Sin ta kafa tare da kasashen Afirka, kuma ya dace bangarorin biyu su kara fahimtar ayyukan da za su yi, da sanya muhimman ra’ayoyi iri daya da aka cimma tsakanin shugabannin kasashen biyu a gaban komai, da daukar matakai a zahirance don kara cimma nasarori.

Shi kuma minista Tuggar ya yaba sosai da nasarorin da aka cimma a zaman taron na wannan karo, inda ya ce, Najeriya tana fatan ci gaba da zurfafa fahimtar juna da kasar Sin, don cimma karin nasarori a hadin-gwiwarsu a fannoni daban-daban.

Bayan taron, bangarorin biyu sun fitar da sanarwa cikin hadin-gwiwa game da cikakken zamansu karo na farko. (Murtala Zhang)