logo

HAUSA

Gwamnatin jihar Gombe ta samar wa manoman jihar takin zamani a kan ragin farashin kaso hamsin

2024-06-21 09:15:44 CMG Hausa

Gwamnatin jihar Gombe ta samar da takin zamani ga manoman jihar a kan ragin farashin kaso hamsin domin gudanar da aikin noman damunan bana.

A lokacin da yake kaddamar da shirin sayar da takin ga manonan a garin Gombe jiya Alhamis 20 ga wata, gwamnan jihar Alhaji Inuwa Yahaya ya ce, an samar da takin ne domin kanana da matsakaitan manoma kadai.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. //////

 

Gwamna Inuwa Yahaya ya yi gargadin cewa gwamnati ba za ta saurarawa duk wanda aka kama yana karkatar da takin zuwa wani waje na daban ba. Ya ce, an samar da takin ne kan ragin kaso hamsin domin karfafa gwiwar manoma su noma wadataccen abinci.

Ya ce, tan dubu arba’in aka samar na taki wanda daga cikin wannan adadi tan dubu 20 ya fito ne daga  gwamnatin tarayyar, sai kuma tan dubu 20 da gwamnatin jiha ta samar, wanda kuma za a sayarwa manoma a kan farashin naira dubu 22 kacal.

“Duk da kalubalen karancin kudi da ake fuskanta a kasa, amma wannan bai kashe gwiwar gwamnati ba wajen saka jarinta mai yawa a bangaren noma, manoma su ne suke da kaso mai yawa na tattalin arzikin dake yankunan karkara a jihar Gombe.” 

Kamar dai yadda gwamnan ya fada, za a sayar da rabin takin ne kai tsaye ga manoma, yayin da kuma raguwar za a sayar da shi ne ta hannun kungiyoyin tsimi da tanadi wato co-operative societies. (Garba Abdullahi Bagwai)