logo

HAUSA

Firaministan Djibouti ya baiwa runkunin tallafin jinya na kasar Sin karo na 22 lambar yabo

2024-06-21 15:01:55 CMG Hausa

 

Jiya Alhamis, firaministan kasar Djibouti Abdoulkader Kamil Mohamed ya baiwa mambobi 12 na runkunin tallafin jinya na kasar Sin karo na 22 lambar yabo ta ranar samun ’yancin kasar.

Kamil ya nuna yabo da godiya ga dukkan mambobin runkunin, kuma yana mai fatan kara hadin kan kasarsa da kasar Sin a fannoni daban-daban, ciki har da kiwon lafiya.

Jakadan Sin dake kasar Hu Bin ya halarci bikin, inda ya ce, lambar yabon da gwamnatin kasar ta baiwa rukunin ya bayyana amincewar gwamnati da jama’ar kasar. Sin za ta ci gaba da hadin kanta da Djibouti a fannin kiwon lafiya da dai sauran bangarori, don ingiza huldar abota bisa manyan tsare-tsare tsakaninsu zuwa wani sabon matsayi. (Amina Xu)