logo

HAUSA

Sin na adawa da takunkumin da Amurka ta kakabawa wasu kamfanoninta bisa zargin hannu a harkokin Rasha

2024-06-20 20:52:19 CMG Hausa

A yau Alhamis ne kakakin ma’aikatar kasuwancin Sin He Yadong ya bayyana a taron manema labarai cewa, kasar Sin na adawa da matakin da Amurka ta dauka na kakabawa wasu kamfanonin kasar Sin takunkumi kan abin da take kira wai shigar wa Rasha. Wannan takunkumin dai ba shi da tushe a dokokin kasa da kasa, kuma bai samu amincewa daga kwamitin sulhu na MDD.

Irin wannan matakin wani hali ne na cin zarafi na kashin kai da kuma matsin lamba ga tattalin arziki, a cewar sa.

Ya kara da cewa, ya kamata bangaren Amurka ya gaggauta dakatar da dakile kamfanonin kasar Sin ba bisa ka'ida ba, yana mai cewa, Sin za ta dauki dukkan matakan da suka dace wajen kiyaye hakki da muradun kamfanoninta ba tare da tangarda ba. (Yahaya)