logo

HAUSA

Xi ya yi rangadi a jihar Ningxia dake arewa maso yammacin kasar Sin

2024-06-20 20:54:08 CMG Hausa

Babban sakataren kwamitin koli na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping, ya yi rangadi a jihar Ningxia mai cin gashin kanta ta kabilar Hui a arewa maso yammacin kasar a jiya Laraba.

Xi ya ziyarci wata unguwar al’umma a birnin Yinchuan, babban birnin jihar, domin ganewa idanunsa yadda rassan jam'iyyar a matakin farko suke gudanar da ayyukansu. Ya kuma ga irin ayyukan da ake gudanarwa a unguwar wajen saukaka rayuwar jama’a da inganta mu’amala tsakanin al’ummar kabilu daban-daban. (Yahaya)