logo

HAUSA

Gwamnan jihar Kano ya kaddamar da aikin titin da ya hade wasu al’umomin yankunan karkara

2024-06-19 09:19:54 CMG Hausa

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya jagoranci kaddamar da aikin tituna masu nisan kilomita 85 da manyan gadoji, wanda aka kiyasta za a kashe naira biliyan 21 wajen kammala su.

Titunan wadanda za su hade al’umomin yankunan karkara da dama, za su taimaka matuka wajen kyautata yanayin rayuwa da na tattalin arzikin mazauna karkara.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Da yake jawabi yayin bikin kaddamar da ayyukan ranar Litinin 17 ga wata, injiniya Abba Kabir Yusuf ya ce, kaddamar da aikin yana daga cikin kashin farko na shirin gwamnatin jihar Kano wajen gina kanana da manyan hanyoyin mota a daukacin yankunan kananan hukumomin dake jihar.

Ya ce, tuni ma ya baiwa shugabannin kananan hukumomin jihar umarnin binciko duk wasu hanyoyin mota da suka shafi filayen noma domin gyara su ko kuma sake ginawa don baiwa manoma damar fito da amfanin gonarsu zuwa kasuwanni cikin sauki.

Gwamnan na jihar ta Kano ya ce, aikin hanyar da ya kaddamar ta farko dai tana da nisan kilomita 70 ne wadda kuma ta taso daga Madobi zuwa Yako zuwa Kafin Mai Yaki wadda wani kamfanin gida zai gudanar da aikin.

“Sai kuma titi na biyu da gada da za a yi muku wanda ta tashi daga Madobi zuwa Kubarachi zuwa Kura shi kuma mun zakulo kamfani na waje na ’yan China wanda dama kwararru ne ba ma a Kano ba ko a Najeriya har a duniya baki daya, wannan kamfani na TEC wannan aiki in Allah ya yarda za su kammala shi cikin wata 18 kacal.”

Aikin titin dai mai nisa kilomita 15 ya kunshi gada mai tsawon mita 200. (Garba Abdullahi Bagwai)