logo

HAUSA

Kasar Sin ta yi kakkausan adawa da yadda Amurka ta tilastawa wasu kasashe murkushe masana'antar sarrafa sassan na’urorin laturoni ta kasar

2024-06-19 20:47:12 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ya ce, bangaren Sin ya yi kakkausar suka ga yadda Amurka ke aiwatar da ayyukan da za su janyowa sauran kasashe da ma kanta lahani.

Kakakin ya bayyana haka ne a gun taron manema labaru da aka saba yi kullum a yau Laraba.

An bayar da rahoton cewa, wani babban jami'in Amurka zai yi balaguro zuwa kasashen Netherlands da Japan, domin neman kasashen biyu da su sanya sabbin takunkumai kan masana'antar sarrafa sassan na’urorin laturoni ta kasar Sin, ciki har da takaita ikon kasar Sin na kera sassan na’urorin laturoni na Chips da ake bukata a fannin fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam.

Kakakin ya kara da cewa, kasarsa tana adawa da arangamar da Amurka ke yi tsakanin bangarori daban daban, wanda har ta kai ga fannin tattalin arziki, kasuwanci, da ma kimiyya da fasaha, kana da tilastawa wasu kasashe murkushe masana'antar sarrafa sassan na’urorin laturoni ta kasar Sin.

Baya ga haka, rahotanni sun ce, a watan Mayun da ya gabata, an yi amfani da jiragen dakon kaya guda 1724 tsakanin kasar Sin da kasashen Turai, inda suka aike da kayayyaki na akwatuna TEU 186,000, wanda ya karu da kashi 14% da kashi 13 cikin 100 a duk shekara, hakan ya kai matsayin koli a wata guda a tarihi.

Game da haka, kakakin ya bayyana cewa, kasar Sin tana son ci gaba da yin hadin gwiwa tare da kasashen da ke kan hanyar "Ziri daya da hanya daya" don kara intanta tattalin arzikin duniya, da kuma amfanar jama'ar kasashen. (Bilkisu Xin)