logo

HAUSA

Kenya ta ce tana samun nasarar yaki da kwararowar hamada

2024-06-18 10:43:01 CMG Hausa

A jiya Litinin ne kasar Kenya ta yi bikin murnar ranar yaki da kwararowar hamada da fari ta duniya, inda ta ce, kasar tana dakile matsalar, kana fadin gandun daji ya zarce kashi 10 cikin kashi 100 bisa baki dayan fadin kasar.

Soipan Tuya, ministar kula da muhalli da gandun daji ta Kenya, wadda ta jagoranci bikin a Laikipia da ke yankin Rift Valley na Kenya, ta bayyana cewa, fadin gandun daji a Kenya ya kai kusan kashi 12.3 cikin kashi 100 bisa baki dayan fadin kasar. (Yahaya)