Chen Wenqing zai kai ziyarar aiki a kasashen Singapore da Afirka ta Kudu
2024-06-18 10:07:09 CMG Hausa
Jiya Litinin, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ya sanar da cewa, bisa gayyatar da aka yi masa, mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin Jam’iyyar Kwaminis ta Kasar Sin, kana babban sakataren kwamitin dokokin shari’ar kwamitin koli, Chen Wenqing zai halarci taron dandalin tattaunawar manyan jami’ai kan harkokin zamantakewar al’umma a tsakanin kasar Sin da kasar Singapore karo na 4 da za a gudanar a kasar Singapore, haka kuma, zai yi ziyarar aiki a kasashen Singapore da Afirka ta Kudu, tsakanin ranakun 18 zuwa 25 ga watan. (Maryam Yang)