Sama da sojojin Burkina Faso 100 ne aka kashe a harin da wata kungiyar al-Qaida ta kai
2024-06-17 10:00:54 CMG Hausa
Wata kungiya reshen al-Qaida ta dauki alhakin wani kazamin harin da aka kai a ranar Talatar da ta gabata, wanda ya yi sanadiyar mutuwar sojojin Burkina Faso sama da 100 a garin Mansila da ke arewa maso gabashin kasar, a cewar kafar sa ido kan masu fafutukar jihadi ta SITE a ranar Lahadi.
Kafar yada labaran kasar ta rawaito wani rahoton da SITE ta gabatar da cewa, wata kungiya mai fafutukar jihadi reshen al-Qaida, Jama'a Nusrat ul-Islam wa al-Muslimin, ta dauki alhakin kai hari a yankin Mansila da ke kusa da kan iyaka da Nijar.
Hakazalika, kungiyar dalibai ta Mansila a cikin wata sanarwar da ta wallafa a ranar Asabar a shafinta na Facebook, ta ce "wasu masu mugun nufi" sun kai hari a sansanin sojoji da gidaje da shaguna a ranar Talata.
Kawo yanzu dai gwamnatin Burkina Faso ba ta fitar da wata sanarwa kan harin ba. (Yahaya)