Binciken CGTN: An yi kira ga kasashe masu ci gaba da su kara daukar nauyin da ya dace kan matsanancin yanayi da ake samu a kai a kai
2024-06-17 18:33:28 CMG Hausa
Ci gaban yanayin zafi a Indiya, da tsananin fari a Spaniya, da ambaliya a Jamus, da yanayi mai tsauri a sassa da dama na kasar Sin ......Matsanancin yanayi na kara muni a fadin duniya. A cewar wani binciken sauraron ra’ayin al’umma da kafar CGTN ta gudanar ta yanar gizo, kusan kashi 86.28 cikin 100 na wadanda suka amsa tambayoyin binciken sun yi kira ga kasashen da suka ci gaba da su dauki karin nauyi da kuma mayar da martanin da ya dace kan sauyin yanayi a duniya.
Idan aka zo kan abubuwan da ke haifar da matsanancin yanayi, wasu masana sun yi nuni da cewa sauyin yanayi a duniya shi ne tushensa. A cikin binciken, kashi 85.08 cikin 100 na wadanda suka amsa tambayoyi sun yi imanin cewa, babu wata kasa da za ta nesanta kanta daga kalubalen sauyin yanayi, don haka ya kamata dukkan kasashe su hada kai don magance matsalar. Kashi 82.69 cikin 100 daga cikinsu kuma sun yi nuni da cewa, tunkarar sauyin yanayi, ba kawai wani abin da ake bukata na ci gaban tattalin arziki ba ne, har ma ya zama wajibi ga manyan kasashe.
Wannan binciken, wanda CGTN ya wallafa a cikin harsunan Turanci, Spaniyanci, Faransanci, Larabci da Rashanci, ya samu amsa daga mutane 13,112 cikin sa’o’i 24. (Yahaya)