logo

HAUSA

Itatuwan Banyan Biyu Suna Shaida yadda ake gadon tunani tsakanin Xi Jinping da mahaifinsa

2024-06-16 20:51:41 CMG Hausa

A ranar 12 ga watan Maris na shekarar 2000, Xi Zhongxun mai shekaru 87 da iyalinsa suka dasa itacen Banyan tare, a gidansu da ke birnin Shenzhen. A matsayinsa na daya daga cikin manyan jagorori da kuma muhimman wadanda suka soma gudanar da manufar yin gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen waje a lardin Guangdong, Xi Zhongxun ya dasa wannan itacen Banyan don bayyana fatansa na samun wurin zama a wannan yanki don yin gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga waje.

A cikin shekaru fiye da biyu da ya dauka yana aiki a Guangdong, Xi Zhongxun ya jagoranci gudanar da ayyuka da yawa. Jerin sabbin matakan da ya dauka, sun aza harsashi ga lardin na jagorantar yin gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen waje a kasar Sin baki daya.

A farkon manufar yin gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen waje, muhimmin aikin mahaifinsa na jagorantar al'ummar Guangdong wajen 'yantar da tunaninsu da ci gaba da yin gyare-gyare ya yi tasiri sosai ga Xi Jinping.

Wani masanin Amurka ya bayyana cewa, aikin da kasar Sin ta yi na yaki da cin hanci da rashawa, gyare-gyare ne. Gudanar da mulki bisa doka, gyare-gyare ne. Kawar da fatara, shi ma yana cikin gyare-gyare, sake fasalin aikin soji, da sake fasalin jam'iyya da hukumomin gwamnati, dukkansu gyare-gyare ne. Wani masanin da ya gudanar da aikin rubuta daftari kan cikakken zama na uku na kwamitin koli na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18, ya tunatar da cewa, "da ba don aniyar Xi Jinping ba, da zai yi wuya a iya fito da wasu manyan gyare-gyare masu yawa."

A shekarar 2012, bayan babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18, Xi Jinping ya zabi lardin Guangdong a matsayin zango na farko da ya yi rangadin aiki a kananan hukumomi. A wurin shakatawa na Lianhuashan da ke birnin Shenzhen na lardin, ya ajiye kwandon furanni ga gunkin tagulla na Deng Xiaoping, tare da dasa itacen Banyan a filin Shanding.

Yanzu, itatuwan Banyan guda biyu da Xi Zhongxun da Xi Jinping suka dasa daya bayan daya a Shenzhen, sun riga sun girma sosai. Kasar Sin da ta mayar da lardin Guangdong a matsayin mafarin yin gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen waje, bayan samun gagaruman sauye-sauye a kasar, yanzu tana kokarin tsara wani sabon tsari na raya kasa mai mulkin gurguzu ta zamani a dukkan fannoni, tare da kokarin cimma babban buri na gina kasa mai karfi da farfado da al'umma. (Bilkisu Xin)