logo

HAUSA

Shugaban Benin ya dauki matakin hana fitar wasu kayayyakin abinci zuwa Nijar, Togo, Mali, Burkina Faso tare da wasu kasashen shiyyar Afrika

2024-06-16 17:24:09 CMG Hausa

Shugaban kasar Benin Patrice talon, ya dauki tsauraran matakan hana fitar da wasu kayayyakin abinci zuwa kasashen Nijar, Togo, Mali, Burkina Faso da kuma wasu kasashen shiyyar yammacin Afrika.

Shugaba Talon ya sanar da daukar matakin ne a jiya Asabar, inda kafofin watsa labarai na kasar suka ruwaito cewa, gwamnatin ta dauki matakan ne bisa la’akari da tashin gauron zabo na farashin kayyayakin abinci.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.

Wannan wani sabon mataki ne karara da ya fito daga wani kuduri tun na taron ministoci na ranar 7 ga watan Yunin shekarar 2024, da ke hana yanzu fita daga kasar Benin da kayayyakin masarufi na bukatun tushe na al’umma.

Ayar doka mai lambar 2024051 da ministocin gwamnatin Patrice Talon da dama suka sanya ma hannu, da ke fitowa karara da wani hanin fitowa da duk kayan abinci daga kasar Benin har tsawon watanni 6.

An hana a tsawon wani wa’adi na watanni 6, fita daga dukkan fadin kasar Benin, cimaka kamar su doya, rogo, dankalin Hausa, da wasu abubuwan da ake sarrafawa daga wadannan sayun abinci, musammun ma kamar garin masara da garin rogo, in ji sanarwar hukumomin kasar Benin. (Mamane Ada)