logo

HAUSA

Gwamnatin Najeriya ta ce za ta kara bullo da tsare-tsaren kyautata rayuwar mutanen da suke tsare a gidajen gyaran hali

2024-06-15 14:26:37 CMG Hausa

Gwmanatin tarayyar Najeriya ta ce zata ci gaba da bullo da sabbin matakan da zasu kara inganta rayuwar dinbun mutanen da suke a tsare a gidajen gyara hali dake sassan kasar daban daban .

Ministan hakokin cikin gida Mr. Olubunmi Tunji-Ojo ne ya tabbatar da hakan ranar Alhamis 13 ga wata lokacin da ya kai ziyara babban gidan gyaran hali na zamani da aka gina a yankin Janguza dake jihar Kano, ya ce mutanen da suke a tsare bisa umarnin hukumomi suna da hakkin a kula da rayuwar su kamar kowanne dan kasa.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Ministan ya ce daga cikin irin wadannan matakai da gwmanati za ta dauka sun hada da kara daukaka matsayin daukacin gidajen yarin dake kasar ta hanyar samar da ababen more rayuwa da samar da damarmakin yin karatu ga daurarrun.

Ministan harkokin cikin gidan na Najeriya ya shaidawa manema labarai cewa ya zo Kano ne domin duba wannan katafaren gidan gyaran hali da aka gina mai cin mutane har dubu 3, inda ya yaba mutuka bisa yadda aka samar da bangarorin koyon sana'o'i, da wuraren ibada, da wuraren wasanni, da kotunan shari'a, kana da asibiti mai gadaje 50.

Mr. Olubunmi Tunji-Ojo ya ce fasalin ginin ya yi daidai da manufar gwamnatin shugaba Tinubu wajen rage cunkoso a gidajen gyaran hali dake kasar ta hanyar hanzarta yanke hukunci daga bangaren alkalai.

"Yana daga cikin burin wannan gwamnati samar da sauki rayuwa ga kowanne dan Najeriya, a saboda haka su ma mutanen da ake tsare da su a gidajen gyaran hali 'yan kasa, a don haka ba za a kyale su ba. "

Yayin ziyarar, ministan yana tare da kontrola janaral na hukumar lura da gidajen gyaran hali ta kasar, Alhaji Halliru Nababa, da sauran jami'an ma'aikatar.(Garba Abdullahi Bagwai)