logo

HAUSA

Ma’aikatar cinikayyar Sin: Sin na da hakkin shigar da kara gaban WTO kan sabbin harajin EU kan EVs na Sin

2024-06-14 10:46:04 CMG Hausa

A jiya Alhamis ne ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin ta bayyana cewa, Sin tana da hakkin shigar da kara a gaban hukumar cinikayya ta duniya wato WTO dangane da shirin kungiyar Tarayyar Turai wato EU na dora harajin wucin gadi kan shigo da motoci mai amfani da wutar lantarki na kasar Sin wato EVs.

Shirin da bangaren Turai ya yi a baya-bayan nan ba shi da tushe na gaskiya da na shari’a, kamar yadda kakakin ma’aikatar He Yedong ya shaida wa taron manema labarai.

Kakakin ya kuma bayyana cewa, matakin ba wai kawai ya gurgunta hakkoki da muradun masana’antar EV na kasar Sin ba, har ma yana kawo cikas ga hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Turai a fannin samar da motoci masu amfani da sabbin makamashi, da hargitsa tsarin masana’antun kera motoci da tsarin samar da motoci na duniya gami da na EU.

Irin wannan mataki shi ne "kariya karara", wanda kuma ake zargin cewa, ya saba wa ka'idojin WTO, Sin za ta dauki dukkan matakan da suka dace don kare hakki da muradun kamfanonin kasar Sin. (Yahaya)