logo

HAUSA

Jami’iyyar ANC mai mulki a Afirka ta kudu ta cimma yarjejeniyar kafa gwamnatin hadin kan kasa da jam’iyyun adawa

2024-06-14 20:18:10 CMG Hausa

Jami’iyyar ANC mai mulki a Afirka ta kudu, ta cimma yarjejeniyar kafa gwamnatin hadin kan kasa tare da jam’iyyar adawa ta DA.

A cewar kamfanin watsa labaran kasar SABC, gwamnatin hadin kan kasar za ta kuma kunshi karin jam’iyyun adawa, da suka hada da PA da kuma IFP.

A daya bangaren, babban kamfanin jarida na “Sunday Times” dake Afirka ta kudun, ya bayyana cewa, za a zabi shugaban kasar mai ci Cyril Ramaphosa, a matsayin sabon shugaban kasar, da tallafin jami’iyyar adawa ta DA nan gaba da yammacin Juma’ar nan. (Saminu Alhassan)