Ding Xuexiang zai halarci taron muhalli da yanayi na Sin da Turai
2024-06-14 21:10:55 CMG Hausa
Bisa shirin da bangarorin Sin da kungiyar kasashen Turai EU suka tsara, Ding Xuexiang, mataimakin firaministan kasar Sin, zai halarci hedkwatar kungiyar EU dake birnin Brussels na kasar Belgium, don jagorantar taron tattaunawar manyan jami'ai, kan batutuwan muhalli da yanayi karo na 5 na Sin da Turai, gami da ziyarar aiki a kasar Luxembourg, tsakanin ranar 17 zuwa 21 ga watan Yunin da muke ciki. (Bello Wang)