logo

HAUSA

Sin na maraba da goyon bayan duk wani kokari da zai taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya

2024-06-14 19:55:32 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Lin Jian, ya gudanar da taron manema labarai na yau da kullum a yau Jumma’a, inda ya yi tsokaci game da taron kolin zaman lafiya na Ukraine, wanda za a gudanar a kasar Switzerland, yana mai cewa kasar Sin tana maraba, da goyon bayan duk wani kokari da zai taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya.

Game da halin da ake ciki a zirin Gaza kuwa, Lin Jian ya ce kasar Sin za ta ci gaba da yin aiki tare da bangarorin da abin ya shafa ba tare da bata lokaci ba, ta yadda za a sa kaimi ga tsagaita bude wuta cikin sauri.

Game da katsalandan da Amurka da Birtaniya, da sauran kasashe ke yi wa harkokin dokokin yankin musamman na Hong Kong na kasar Sin kuwa, Lin Jian ya ce, harkokin yankin Hong Kong na cikin gidan kasar Sin ne kadai, kuma ba za a amincewa ko wane sashe ya tsoma baki cikin su ba.

Game da taron tattaunawar muhalli da yanayi karo na 5 na Sin da Turai da za a kira, Lin Jian ya ce, Sin da Turai suna cimma moriyar juna, da kuma yin hadin gwiwa da yawa, a fannin samun ci gaba ba tare da gubata muhalli ba.  (Safiyah Ma)