Firaministan kasar Sin ya isa New Zealand don ziyarar aiki
2024-06-13 09:51:16 CMG Hausa
Firaministan kasar Sin Li Qiang ya isa kasar New Zealand yau Alhamis domin gudanar da ziyarar aiki, wannan shi ne zango na farko na ziyarar aiki da zai yi a kasashe uku farawa daga yau ranar 13 zuwa 20 ga wannan wata.
A yayin ziyarar nasa, Li zai yi musayar ra’ayi mai zurfi tare da babbar gwamna madam Cindy Kiro, da firaministan kasar Christopher Luxon da sauran jami’ai kan dangantakar dake tsakanin Sin da New Zealand, da kuma batutuwan kasa da kasa da na shiyya-shiyya da suka shafe su.
Haka zalika, Li zai kuma kai ziyarar aiki a kasashen Australia da Malaysia, kuma zai jagoranci taron shekara-shekara na shugabannin Sin da Australia karo na tara tare da firaministan Australia Anthony Albanese. (Yahaya)