An Fitar Da Shirin Gina Shuwagabannin Jam’iyya Da Gwamnatin Sin Na 2024-2028
2024-06-13 20:19:51 CMG Hausa
Kwanan nan, hukumar zartaswa ta kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, ta fitar da "Shirin gina shuwagabannin jam’iyya da gwamnati na Sin wanda za a aiwatar tsakanin shekarar 2024 zuwa 2028", kuma ta sanar cewa, ana bukatar dukkan yankuna, da sassa su aiwatar da shi da gaske, bisa ainihin halin da suke ciki.
Takardar da hukumar ta fitar ta ce an tsara shirin gina shuwagabannin jam’iyya da gwamnatin Sin, daga 2024 zuwa 2028 ne bisa aikin jam'iyya na sabon zamani.(Safiyah Ma)