An gudanar da dandalin kasa da kasa game da “Tarihi da makomar Xinjiang” a Kashgar
2024-06-12 19:42:04 CMG Hausa
A yau Laraba ne aka gudanar da dandalin kasa da kasa game da “Tarihi da makomar jihar Xinjiang ta kasar Sin” a birnin Kashgar, dandalin da ya mayar da hankali ga yayata musaya, tsakanin sassan kasa da kasa a fannonin gano ababen tarihi dake binne a kasa da tarihi, da ingiza bincike mai fadi tare, game da jihar Xinjiang da tarihin ta, da zurfafa musaya da koyo daga juna, tsakanin wayewar kan Sin da na sauran sassan duniya.
Taron ya hallara sama da kwararru 170, da masana daga Kazakhstan, da Amurka, da Australia, da Masar da sauran kasashe, an kuma tattauna batutuwa da suka hada da fannin binciken ababen tarihi dake binne a Xinjiang, da batun dunkulewar kasar Sin, da hanyar siliki ta yammaci, da musaya, da koyi da juna tsakanin wayewar kan gabashi da yammaci, da ci gaban Xinjiang, da tafarkin kasar Sin na zamanantar da kai. (Saminu Alhassan)