logo

HAUSA

Majalissar zartarwar jihar Jigawa ta amince da kirkirar Kantunan sayar da kayayyakin abinci kan rangwamen farashin kaso 25

2024-06-12 09:13:51 CMG Hausa

Majalissar zartarwar gwamnatin jihar Jigawa dake arewacin Najeriya ta amince da samar da shagunan sayar da kayayyakin abinci a dukkannin mazabu 287 dake jihar.

Kwamishinan yada labaran jihar Alhaji Sagir Ahmad ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a karshen mako jiya jim kadan bayan kammala taron majalissar a gidan gwamnatin jihar. Ya ce, kantunan idan an samar da su  za su rinka sayar da kayayyaki a kan rangwamen farashi na kaso 25.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Tsarin kantunan masu lakabi da shagunan tallafin radadin rayuwa, idan an samar da su za su taimaka matuka wajen wadatar abinci ga jama’a sannan kuma su kawar da talauci.

Kwamishinan ya ce, yana daga cikin makasudin yanke shawarar kirkirar wadannan kantuna karyar da farashin kayayyakin masarufi a dukkannin lungu da sako dake jihar.

Alhaji Sagir Ahmad ya ci gaba da cewa domin tabbatar da wanzuwar wannan shiri, gwamnati ta samar da kwamiti mai wakilai 10 da zai kasance karkashin shugaban ma’aikatan jihar kuma kwamitin ya kunshi kwamishinoni da babban akanta-janaral na jihar da wakilci daga hukumar samar da ayyukan dogaro da kai da samar da ayyukin yi ga matasan jihar.

“Adadin Naira miliyan dari tara da ashirin, da dubu dari takwas da  tamanin da hudu da Naira dari shida da shirin da biyar aka ware domin sayo kayayyakin abinci da jakunkuna na musamman da kuma hayar shaguna, haka kuma za a samar da wuraren cirar kudi ta banki a kantunan domin saukaka harkokin cinikayya ga al’umma za a kuma rinka juya kudaden cinikin ne domin ganin cewa harkoki ba su tsaya ba.”

Daga cikin aikin ’yan kwamitin, fito da tsarin yadda za a tafiyar da kantunan da binciko wuraren da ya kamata a kafa kantunan, sannan kuma da sanya ido wajen ganin wadanda aka samar da kantunan domin su suna cin gajiya yadda yakamata. (Garba Abdullahi Bagwai)