EU na shirin kakaba harajin wucin gadi kan ababen hawa masu amfani da lantarki kirar kasar Sin
2024-06-12 20:34:29 CMG Hausa
Kakakin ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin, ya ce kungiyar tarayyar Turai EU, na shirin kakaba harajin wucin gadi, kan ababen hawa masu amfani da lantarki kirar kasar Sin, wadanda ake shigarwa kasashe mambobin kungiyar ta EU, a wani yunkurin na cike gibin kudaden rangwame da EUn ke zargin an samarwa kamfanonin da suke kera motocin a Sin.
Kakakin, wanda ya yi tsokacin a Larabar nan, ya ce EU ba ta bi ka’ida wajen daukar wannan mataki ba, ta kuma yi watsi da gaskiya, da ka’idojin kungiyar cinikayya ta duniya WTO, kana ta yi watsi da kakkarfar adawar da Sin ta sha yi kan matakin. Kaza lika ta kawar da kai daga kiraye-kiraye, da jan hankali daga gwamnatocin kasashe mambobin EUn masu yawa, da kamfanonin kasashen kungiyar.
Ya ce Sin ta yi matukar damuwa, tare da nuna rashin amincewa da matakin. Tana kuma kira ga EU, da ta gaggauta gyara wannan kuskure, kuma Sin din za ta zura ido sosai kan matakan EUn na gaba, tare da daukar dukkanin matakan da suka wajaba, domin kare halastattun hakkoki, da moriyar kamfanonin ta.
Har ila yau, a dai wannan rana, kungiyar kamfanonin kirar motoci ta kasar Sin, ta bayyana fatan cewa, EU ba za ta siyasantar da batutuwan da suka jibanci tattalin arziki da cinikayya ba, kana ba za ta keta hurumin tsare tsaren cinikayya ba. (Saminu Alhassan)