Xi ya jaddada muhimmancin inganta tsarin kamfanoni na zamani mai halayyar musamman ta Sin
2024-06-11 20:45:00 CMG Hausa
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada muhimmancin inganta tsarin gudanar da harkokin kamfanoni a zamanance mai halayyar musamman ta Sin, tare da yayata samar da muhalli budadde, na yin kyakkyawar takara a fannonin kirkire kirkiren kimiyya da fasaha.
Shugaba Xi ya yi wannan tsokaci ne a Talatar nan, yayin da yake jagorantar taro karo na 5, na hukumar koli ta zurfafa sauye sauye daga dukkanin fannoni, karkashin kwamitin kolin JKS na 20, wanda yake shugabanta. (Saminu Alhassan)